14/04/2026
SHAWARA A GAREKU YAN UWANA MATA MASU SANA'AR DINKI WADAN DA SUKE TASOWA
Assalamu'alaikum barkanku da wannan lokacin, Yau Mam's Clothes Nation inada dan tsokaci akan yan uwana mata masu sana'ar dinki, akwai wadan da suke kukan ce basuda jari, ni a tunanina matsawar kika mallaki Keken dinki to kin mallaki jari, Shawarata karki ki zauna kice sai kin Jira jari sannan kiyi sana'arki, kiyi amfani da abinda k**e dashi ki jajirce Kuma kiyi hakuri, matsawar kikayi hkn da sannu nasara zata zo miki. Ni lokacin dana fara sana'ar Dinki, a cikin sana'ar na samu jari dan lokacin ban fara da abinda ya wuce 2k ba, amma ni a lokacin nayi amfani da social media wajen tallata sana'ata, idan nayi Riga daya ta Yara zan dauka a hoto na na tallata tun ba a tayawa Kuma Hakan bai sa na Karaya na daina ba, na cigaba da tallatawa har hankalin mutane yazo Kai aka fara tayawa, duk Wanda yace yana so bayan ya fadamin adadin da yake so zan sanar da mutum sai ka bani Rabin kudin kaya idan na gama aiki ka cikamin ka karbi kaya, Alhamdulillah 🥰 a haka na tafi da tsarina Kuma Allah ya dafamin Kuma har yanzu a wannan tsarin nake, Dan haka Ina kara Baku shawara ku jajirce kuyi hakuri, sannan ku tafi da zamani ta hanyar amfani da social media Dan a wannan zamanin Social media na taka mahimmiyar rawa wajen kasuwanci.
Allah ya cigaba da saka mana albarka a cikin sana'armu 🤲
Always your outlook is my concern 😊
Maryam Abdullahi Muhammad 🥰